1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwanda ta fara gwajin maganin cutar Marburg

October 16, 2024

A karon farko, Ruwanda ta fara gwajin magungunan cutar Marburg, wadda ta yi sanadin rayukan gomman mutane a kasar Ruwanda.

https://p.dw.com/p/4lqqj
Ruwanda ta fara gwajin maganin cutar Marbug
Ruwanda ta fara gwajin maganin cutar Marbug Hoto: Ulrich Perrey/dpa/picture-alliance

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya, shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce wannan labari ne mai karfafa gwiwa. Ya kuma yaba wa kasar kan kaddamar da fara gwajin cutar Marburg tare da hadin gwiwar hukumar, inda suka sanya maganin Corona a cikin gwajin. Ghebreyesus ya ce, an fara gwaji kan maganin Remdesivir da aka yi amfani da shi a baya wajen magance cutar Covid-19.

Tun da a karshen watan Satumbar shekarar 2024, aka sanar da bullar cutar Marbug a Rwanda inda aka fara rigakafinta a farkon watan Octobar 2024. Ana samun cutar Marburg ne daga jikin Jemage, cutar da ke da alaka da cutar Ebola na saurin halaka mutum idan ya kamu da ita.