1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwanda ta bar sojojinta a Sudan

September 25, 2010

Kimanin sojojin kasar Ruwanda 3500 ke aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Sudan wanda tun can da farko gwamnatin kasar ta ce za ta janyesu

https://p.dw.com/p/PMdM
Shugaban Kasar Ruwanda, Paul KagameHoto: AP

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar Ruwanda ta yanke shawarar barin dakarunta masu lura da aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Sudan.Tun can da farko dai hukumomin na kasar sun yi barazanar janye sojojin nasu .

Rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana ya zargi sojojin kasar ta Ruwanda da aikata kisan kiýasu a gabacin jamhuriyar Kongo. Kasar ta Ruwanda dai na da dakaru kusan 3500 da ke can jibge a Sudan, wacce ke fuskantar barazana barkewar wasu sabbin tashe-tashen hankula, dangane da zaben rabar-gardama da ake shirin gudanar wanda zai baiwa yankin kudancin kasar 'yancin cin kashin kai .

A halin da ake ciki dai hukumomin na Khartum sun ce a shirye suke su amince da duk yadda sakamakon zaben ya kaya .

Mawallafi :Abdourahamane Hassane

Edita : Halima Balaraba Abbas