Ruwan sama ya haddasa ambaliyar ruwa | Zamantakewa | DW | 20.09.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ruwan sama ya haddasa ambaliyar ruwa

Sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu cikin 'yan kwanakin nan kasashen Najeriya da Nijar sun fuskanci ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyyar rayuka da gidaje da wuraren ibada da na kasuwancin jama’a.

Yanzu haka jama’a da dama na cikin wani mawuyacin yanayi bayan da suka yi asarar gidajensu da ma dukiyoyi masu tarin yawa, lamarin da ya jefa su cikin kaka-ni-ka yi. Kimanin gidaje dubu daya da tara ne dai wannan ambaliya ta lalata yayin da wuraren kasuwancin jama’a da na ibada da suka hada da masallatai da coci adadinsu ya kai sittin da bakwai da wannan ambaliya ta shafa.

Sauti da bidiyo akan labarin