Ruwan sama sun kashe mutane 78 a China | Labarai | DW | 23.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ruwan sama sun kashe mutane 78 a China

Rahotanni daga China na cewa mutane 78 sun hallaka a yayin da wasu 500 suka jikkata a sakamakon wasu ruwan sama kamar da bakin kwarya da kankara da aka yi a birnin Jiangsu na Gabashin kasar.

China Hochwasser

Kamfanin dillancin labaran kasar ta China ya ruwaito cewar ruwan saman ya kuma tafi da gidaje da dama a birnin Yancheng. Yankunan kasar ta China da dama ne dai suka fuskanci ruwan sama mai tsananin gaske a wannan mako.

Abin da ya haddasa asarar rayuka da dama, da ta kadarori da aka kiyasta darajarsu a miliyan 410 na Dalar Amirka, a yayin da mutane dubu 200 suka rasa muhallansu.