Ruwa ya yi ɓarna a ƙasar Mali | Labarai | DW | 29.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ruwa ya yi ɓarna a ƙasar Mali

Ambaliyar ruwa ta yi awan gaba da rayukan mutane 23 tare da lalata gidaje da dama a ƙasar Mali. Sai dai wasu sun ki ƙaurace wa matsugunansu duk da halin da ake ciki.

default

Kasashen Afirka da dama ciki har da Mozambik sun fuskanci ambaliya

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe sa'o'i ana shatatawa a ƙasar Mali ya hallaka mutane akalla 23 tare da lalata gidaje da dama. Ma'aikatar da ke kula ayyukan jin kai ta wannan ƙasa ta nunar da cewa unguwannin ya ku bayi na birnin Bamako na daga cikin wuraren da ambaliyar ta fi barna.

Kafar telebijin mallakar gwamnatin Mali ta nuna hotunan mutanen da ruwa ya zo musu iya wuya, yayin da gidajensu kuwa suka nitse. 'Yan kwana-kwana da sauran jama'a na ci gaba da kai ɗauki ga mutanen da suka rasa matsugunansu. Tuni ma dai hukumomin suka tanadi sansanoni uku da za su tsugunar da waɗanda ambaliyar ta shafa. Kazalika ta jibge borguna da gidan sauro da sauran kayayyakin matsarufi da suke bukata.

Sai dai har yanzu wasu daga cikin waɗanda ambaliyar ta shafa suna ci gaba da yin kunnen uwar shegu game gargaɗin da aka yi musu na ƙaurace wa matsugunansu saboda ruwan saman da ke sauka da ƙarfi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdourahmane Hassane