1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruto da M23 sun dauki hankalin jaridun Jamus

September 13, 2013

A daidai lokacin da aka fara shari'ar mataimakin shugaban Kenya, William Ruto a kotun ICC jaridun Jamus sun nuna hakan a matsayin gwada yar kashi tsakanin sa da kotun

https://p.dw.com/p/19hCs
William Ruto a kotun ICCHoto: AP

Jaridun na Jamus sun gabatar da sharhuna asu tarin yawa game da nahiyar Afirka a wannan mako mai karewa, to amma wadanda suka fi daukar hankali sune shari'ar da aka fara, aka kuma dakatar ta mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto a gaban kotun kasa da kasa dake birnin The Hague, sai kuma kokarin cimma zaman lafiya a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, inda shugabannin kasashen yankin tsakiyar Afirka suka yi taro a Kampala kan rikicin yan tawaye a gabashin kasar ta Congo.

A farkon wannan mako ne kotun shari'ar masu aikata manan laifuka ta kasa da kasa a birnin The Hague ta fara shari'ar mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto, wanda ake tuhumarsa da laifin kisan kare dangi, tattare da tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki a Kenya din a shekara ta 2007. A wannan lokaci an yi kiyasin cewar mutane akalla 1200 ne suka rasa rayukan su sakamakon tashin hankalin, mafi yawansa na kabilnci. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace a lokacin da aka fara shari'ar, maimakon William Ruto yayi nadamar laifin da aka ce ya aikata na kara hura wutar tashin hankalin, sai ma ya maida kansa a matsayin wanda aka yiwa laifi. Masu gabatar da kara sun zargi Ruto, wanda ya fito daga yankin Eldoret kuma dan kabilar Kalenjin da laifin bada umurnin kisan daruruwan yan kabilar Kikuyu da kuma koran dubbai daga yankunansu na asali.

Ita ma jaridar Berliner Zeitung ta tabo wannan shari'a, wadda tace zata zama kamar dai gwada yar kashi ce tsakanin kotun ta kasa da kasa da William Ruto. Saboda haka ne a jawabinta na bude karar kan mataimakin shugaban na Kenya, lauyar kotun, Fatouma Bensouda tace tana tuhumarsa ne da laifin kisan kare dangi da gallazawa wadanda ba yan kabilarsa ba da kuma maida yan kabilar Kikuyu yan gudun hijira. Bayan wannan kisa ne janar sakatare na majalisar dinkin duniya, a wancan lokaci, Kofi Annan ya nada wani kwamitin bincike da ya gano cewar manyan yan siyasa da yan jarida da manyan jami'an gamnati suna da hannu a kisan dubban mutane a shekarar ta 2007. Shari'ar ta Ruto an fara ta ne a daidai lokacin da Kenya tace zata fice ma daga kotun ta kasa da kasa da ake kira ICC a takaice. Jaridar Berliner Zeitung tace yin haka zai shigar da wani sabon zamani ga aiyukan kotun, tare da tsoron Kenya din tana iya zama abin koyi daga kasashen Afirka da dama dake nuna rashin gamsuwarsu da aiyukan kotun.

A kasar Kongo, gwamnati tana ci gaba da gwagwarmayar neman kawo karshen aiyukan yan tawaye na kungiyar M23 a gabashin kasar. Dangane da haka, jaridar Die Tageszeitung tyi sharhi inda tace shugabannin kasashen Jamhuriyar Democradiyar Kongo da na Ruwanda da Yuganda da Tanzaniya sun tattauna tsakaninsu a Kampala kan yadda za a kawo karshen tawayen na kungiyar M23. Jaridar tayi tsokaci da cewar ba a saba ganin haduwar wadannan shugabanni wuri guda domin nazarin al'amuran da suka shafi yankinsu ba, saboda zargin juna da laifin goyon bayan yan tawaye a kasashen juna. Shugabannin sun kuma gaiyaci wakilan kungiyar M23, tare da fatan jan hankalin su ga komawa shawarwarin zaman lafiya tare da shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Joseph Kabila.

Kenia Prozess gegen William Ruto Kriegsverbrechen Symbolbild
Tashin hankalin kabilanci a Kenya bayan zaben shekara ta 2007Hoto: picture-alliance/AP Photo

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Usman Shehu Usman