Rundunar tsaro ta JTF ta kame wasu yan ƙungiyar boko haram a Najeriya. | Labarai | DW | 03.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar tsaro ta JTF ta kame wasu yan ƙungiyar boko haram a Najeriya.

Rundunar ta tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar Borno da ke a yankin arewacin Tarrayar Najeriya, ta ce ta kashe wasu data bayyana ‘yan kungiyar Boko haram su guda 20.

Rundunar ta ce ta kashe yan' bindigar ne bayan wani hari da dakarunta suka kai a barakin Sojoji da ke Mongunu ,da ke da nisan Kilomita 200 daga Maiduguri kan iyaka tsakanin Cadi da Kamaru.

Kakakin rundunar laftanar kanar Sagir Musa ya shaidawa manema labarai cewar sun samu nasarar gano wasu muggan makamai da abbaban hawa da aka nufi kai wannan harin da su, wanda bai sami nasara ba.Haka kuma rundunar ta ce ta kame wasu jigajigan ‘kungiyar da suka kitsa kai hari Maiduguri bayan kammala taron gwamnonin.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu.