Rundunar sojin Jamus ta fara horas da sojojin Mali | Labarai | DW | 29.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar sojin Jamus ta fara horas da sojojin Mali

A wani mataki na gaggawa rundunar Jamus ta Bundeswehr ta fara aikin horas da sojojin Mali, a wani bangare na aikin tawagar EU da za a kawashe watanni 15 ana yi.

A wannan Litinin rundunar sojin Jamus wato Bundeswehr ta kaddamar da aikin horas da takwarorinta na rundunar sojojin kasar Mali, inda za a koyar da su dubarun yaki da masu kaifin kishin addini dake arewacin kasar. Ya zuwa yanzu dai sojojin kasar ta Mali ba su da wata kwarewa kana kuma suna fama da karancin kayan aiki musamman na zamanai. A farkon wannan shekara sojojin Faransa suka kaddamar da yakin fatattakar sojojin sa kai na Musulmi, da suka mamaye arewacin Mali bayan juyin mulkin da soji suka yi. A ziyarar da ya kai birnin Bamako a baya, ministan tsaron Jamus Thomas de Maizire yayi karin haske game da aikin sojojin kasarsa a Mali.

"Za a samu kyakkyawan aikin ci gaban kasa a lokaci mai tsawo, da zarar sojojin Mali sun karbi ragamar tabbatar da tsaron kasar. A nan kuwa za mu ba da gudunmawa ta hanyar ba su horo."

Sojojin Jamus kusan 330 wani kuduri ya amince da tura su, daga cikinsu akwai masu horaswa 40 da kuma masu aikin jiyya guda 40.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Sale Umar Saleh