Rundunar sojin Amurka tace tana tsare da matan Iraqi biyu | Labarai | DW | 19.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar sojin Amurka tace tana tsare da matan Iraqi biyu

Rundunar sojin Amurka a kasar Iraqi tace tana tsare da fursunoni mata guda 8,bayan da wadanda suka sace wata yar jaridar kasar Amurka sunyi barazanar kashe ta muddin dai sojin Amurkan basu sako dukkan matan Iraqi da suke tsare da su ba cikin saoi 72.

Kakakin rundunar sojin Amurkan,Lt.Aaron Henninger,yace sun atsare da matan ne bisa laifin barazana ga tsaron.

A dai ranar 7 ga watan janairu aka sace Jill Carroll da take aikin jaridar mujallar Christian science monitor a kasar Amurka.

Yanzu haka dai ana ci gaba da yin kira ga wadanda suka sace ta da su gagauta sako ta.

A halin da ake ciki kuma,wata kungiyar musulmi daga kasar Amurka ta fara kokarin ganin an sako wannan mata,inda kungiyar ta musulmi ta shirya gudanar da wani taron manema labarai a yau a Amman na kasar Jordan,da kuma wani taron a gobe jumaa a Bagadaza.

Yanzu haka rahotanni dake shigowa sunce maaikatar tsaro ta Iraqi ta ce zaa sako 6 daga cikin matan Iraki da ake tsare da su,amma tace sake sun ba shi alaka da bukatun wadanda suka sace matar.