Rundunar NATO ta kashe farar hula a Afganistan | Labarai | DW | 08.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rundunar NATO ta kashe farar hula a Afganistan

An hallaka fararan hula aƙalla guda goma a gabashin Afganistan a wani farmakin da jiragen sama na yaƙi marasa matuƙa na Rundunar suka kai.

Wani babban jami'an 'yan sanda a garin Kunar da ke kan iyaka da Pakistan, inda 'yan Taliban ke da sansani ,ya ce harin ya yi kaca-kaca da wata motar ta farar hula sannan ya ce harin ya rutsa da mata da yara. Jamian na rundunar ta sojin ISAF sun ce ,sun yi saitin harin ne, a kan yan Taliban amma kuma aka samu wannan kuskure.

A cikin watan Maris da ya gabata shugaba Hamid Karzai ya gargaɗi Amirka da ta daina kai hare-hare da jirage marasa matuƙa a ƙasarsa, a sakamakon wani harin da ya haddasa mutuwar mata guda goma haɗe da yara ƙanƙana a garin Kunar. Wasu rahotannin kuma da ke zo mana daga Afganistan ɗin na cewar 'yan ƙungiyar Taliban sun kashe wasu jami'an hukumar leƙen asiri na ƙasar guda huɗu a wani harin da suka kai a wani ofishin hukmar da ke a kudancin ƙasar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman