1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An kafa hukumar jami'an shirin ko-takwana

January 9, 2020

An kaddamar da jami'an shirin ko-takwana a Kudu maso Yammacin Najeriya don yaki da munanan tabi'u kamar garkuwa da mutane da fyade ga yara mata ko sace-sace.

https://p.dw.com/p/3VxZZ
Nigeria Polizei in Lagos
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Wannan tsari na kafa jami'an shirin ko-takwana ana kiransa Amotekun a harshen Yarbanci wato damisa ke nan da Hausa. A birnin Ibadan aka tabbatar da hedkwatar hukumar, inda jihohi shida na Kudu maso Yammacin Najeriya suka bada tallafi na ababan hawa da kudade don aikin jami'an ko-takwanan.

Yayin kaddamar da wannan hukuma kuwa, ta samu sahalewar hukumar 'yan sanda ta kasa, inda za su tafi kafada da kafada don cimma manufa. Mai martaba Oba Kuta Makama, sarkin yanka a Jihar Osun, ya ce za a iya samun nasara mai amfani bisa hadin gwiwa da rundunar 'yan sandan Najeriya.

"Babu bambanci tsakanin Amotekun da Civilian JTF. An dauki mutane ne da suka san yankin, suka san kowane lungu a dukkan jihohin yammacin Najeriya. Dukkansu kuma sanannu ne da aka dauko su daga kananan hukumomi da suka fito, mu kanmu sarakuni mun san wasu daga cikinsu."

Al'umma a yankin sun nuna farin ciki da kirkiro da wannan tsari domin a ganinsu za su bada gudunmawa wajen kakkabe yankin daga masu munanan tabi'u. Sun yi fata sabbin jami'an ko-takwanan da za su yi aiki tare da 'yan sanda, za su taimaka a kawo karshen cin hanci da ake zargin 'yan sanda na karba daga masu aikata laifi, su kuma sake su ba tare da an yi musu hukunci ba.