Rugujewar tasirin Amirka a Gabas ta Tsakiya | Labarai | DW | 21.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rugujewar tasirin Amirka a Gabas ta Tsakiya

Mataimakin shugaban kasar Mike Pence ya bayyana cewa shi da Sarki Abdullah na kasar Jordan sun amince da sabanin da ke tsakaninsu a bisa matsayin birnin Kudus

A yanzu dai kasar ta Amirka ta riga da ta amince da Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila. Mike Pence ya fadi sabanin da ke tsakaninsu da Jordan ne a wannan Lahdi, bayan kammala ziyarar da ya kai a kasar.Tun gabanin ziyarar ta mataimakin shugaban kasar Amirka ne dai, Sarki Abdullah ya yi gargadin cewa matakin na shugaba Donald Trump, ya kawo rudani a yankin Gabas ta Tsakiya baki daya, kuma hakan ya kara kunna wutar da za ta ingiza masu tsatsauran ra'ayi. Inda Sarkin ya kara da cewa hakan kuwa ya kara jefa sasantawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Larabawa cikin rudani. Tuni dai mataimakin shugaban kasar Amirka Mike Pence ya isa Isra'ila a ci gaba da ziyarar da yake yi a kasashen Larabawa. Tun da jimawa ne dai aka shirya ziyarar amma aka jinkirata ta, biyo boren kasashen laraba kan sauya matsayin birnin Kudus, abin da ya kai ga shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, ya soke ganawarsa da Mike Pence wanda aka shirya yi tun gabanin ayyana Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila.