1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bene ya rufta da mutane a Amirka

Abdul-raheem Hassan
June 28, 2021

Masu agaji na cigaba da neman sama da mutane 150 da suka bace bayan mutuwar mutane da dama a ruftawar dogon bene a jihar Florida, yayin da 'yan uwa da dangin mamata ke cikin alhini.

https://p.dw.com/p/3viBJ
Weltspiegel | Miami, USA | Eingestürztes Hochhaus
Hoto: Giorgio Viera/AFP/Getty Images

Akalla mutane 10 aka tabbatar da mutuwarsu bayan ruftawar dogon bene mai hawa 12 a jihar Florida na kasar Amirka, rahotanni na cewa akwai mutane masu yawa da ake nema haryanzu.

'Yan sanda sun tabbatar da tantance gawar wasu tsoffin ma'aurata 'yan asalin Venezuella masu alaka da yahudawa mazuana Florida da Chicago, yanzu haka ma'aikatan agaji na cigaba da tono mutanen da gini ya binne a yakin da lamarin ya faru.