Rufe taron WTO | Labarai | DW | 19.12.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rufe taron WTO

HONG KONG

Ministocin cikin daga kasasge 149 dake da wakilci a kungiyar ciniki ta duniya,sun kammala mahawararsuz ta yini shida a birnin Hong kong A jiya inda suka kare tattaunawar daga rushewa ,da yar kwarya kwaryar yarjejeniya na kawo karshen harajin kayayyakin amfanin gona dake shiga kasuwannin a shekara ta 2013,tare da bude kasuwannin kasashe masu cigaban masanaantu wa kasashe matalauta.

Duk dacewa babu wata nasara da wannan taro ya cimma.Ministocin sun bayyana farin cikinsu na kareta daga rushewa kamar yadda ya wakana a birnin Seattle a 1999.da Cancun 2003.

Wakilan sun dai bayyana shakku dangane da yiwuwan cimma nasaran tattaunan na shekaru 4 kafin nanda kashen shekarata 2006,inda bayan nan shugaba George W Bush na Amurka ka iya rasa ikonsa na tattaunawa harkokin ciniki a majalisar kasar.

Wakilin Amurka a zauren taron Rob Portman ya jaddada bukatar cimma yarjejeniya kan harajin kayayyakin gona,domin cimma yarjejeniyar ta 2006.

Shi kuwa Komishinan ciniki na kungiyar EU Peter Mandelson ya bayyana taron dacewa babu nasara da aka samu,kodayake an ceci taron daga rushewa.

A yayinda kasashen Afrika ke ganin cewa an tabka mahawara na kwanaki 6 ba tare cimma wani tudun dafawa,akan yadda kasashe masu arziki zasu bude kasuwaninsu domin kasashe matalauta suci gajiyarsu ba.

To saidai Babban Directa na kungiyar ciniki ta duniya Pascal Lamy ,ya fadawa ministocin cinikin cewa sun dan farfado da fatan cewa zaa samu bunkasar tattalin arziki nan gaba,tare da ceton milliyoyin mutane daga kangi na talauci ,ta hanyar sanya musu rangawame wajen shigar da kayayyakin gonansu kasuwanin turai.

 • Kwanan wata 19.12.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu7k
 • Kwanan wata 19.12.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu7k