Rudani kan siyasar kasar Burkina Faso | Siyasa | DW | 07.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rudani kan siyasar kasar Burkina Faso

Babu tabbas a kasar Burkina Faso a game da wadanda za su jagoranci gwamnatin wucin gadi ta kasar, bayan faduwar gwamnatin Blaise Compaore

Har kawo yanzu babu tabbas a kasar Burkina Faso a game da wadanda za su jagorancin gwamnatin wucin gadi ta kasar, bayan faduwar gwamnatin Blaise Comapore a makonni da suka gabata, duk kuwa da gargadin da kungiyar Tarrayar Afirka ta yi ga shugaban gwamnatin mulkin soji Lt Kanar Yacouba Isaac Zida cewar ya mika mulkin ga farar hula a cikin makonnin da ke tafe, da alama an shiga rudani a kasar na sabanin da ke tsakanin 'yan siyasar da kungiyoyin fararen hula a kan batun kafa gamnatin rikon kwaryar.

Kalubalen da 'yan siyasa da kungiyoyin fararen hula a Burkina Faso suke fuskanta a kan maganar kafa gwamnatin rikon karya, wanda tun kafin yin boran da ya share gwamnatin ta Blaise Compaore 'yan siyasar ba su tsara makomar gwamnatin wucin gadin da kuma yadda za ta kasance, kamar yadda Koffi Amétépé, editan wata mujallar a kasar ta Burkina Faso ya bayyana.

Sai dai cewar wani kwamiti da aka girka wanda ya hada wakilan 'yan siyasa da kungiyoyin farar hula da kuma sarakuna gargajiya na tattauna wani tsari na yadda gwamnatin rikon kwarya za ta kasance da kuma mutanen da suka cancanta a zaba.

Duk da haka akwai jan kafa a cikin lamarin wanda wasu suke tunani cewar a maimakon a wakilta 'yan siyasa ko wakilan kungiyar farar hula abin da ya fi shi ne a mika jagorncin gwamnatin ga shugabannin addinai.

Desire Boniface wani mai limanci a jami'ar birnin Wagadugu ya ce dama 'yan majami'ar Katolika sun taba rike wani matsayi a baya na aikin gwamnatin na bincike.

Sauti da bidiyo akan labarin