Ruɗanin sakamakon zaɓe a Afghanistan | Siyasa | DW | 10.09.2009
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ruɗanin sakamakon zaɓe a Afghanistan

Zargin maguɗi da aringizon ƙuriú na sanya shakku a game da sahihancin sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Afghanistan.

default

Madugun Jamíyar adawa a Afghanistan Dr Abdullah Abdullah, ke jawabi ga taron magoya bayansa a birnin Kabul game da sakamakon zabe.

Har yanzu baá kammala ƙidayar dukkanin ƙurin ba tukunna. A halin da ake ciki hukumar zaɓen ta baiyana sakamakon kashi 92 na adadin ƙuriún da aka kaɗa. Abu guda dai da aka haƙiƙance shine cewa mai yiwuwa Hamid Karzai ya cigaba da riƙe muƙaminsa na shugaban ƙasa bisa nasarar da ya samu ta kashi 54 cikin ɗari na adadin ƙuriún da aka kaɗa. Ko da yake hukumar zaɓen ta ce an sami kurakurai, a ranar Talatar da ta wuce ma ta sanar da ƙin amincewa da wasu ƙuriú kimanin 200,000 waɗanda ta baiyana cewa sun lalace. Shugaban tawagar sa ido na ƙungiyar tarayyar turai akan zaɓen Dimitri Loannou shima ya baiyana rashin jin daɗi da wannan maguɗin.

Maguɗin zaɓe ko kuma rashin ingantattun bayanai, makonni uku bayan zaɓen na ranar 20 ga watan Augusta, ya zuwa yanzu ya sami ƙorafe ƙorafe har guda 2200. Zarge zargen da aka taállaka da yan takara 38 da suka shiga zaɓen. Alal misali akwai raɗe-raɗin cewa da uwan Karzai Ahmed Whali an sami shi dumu dumu ya cika akwatin zaɓe da ƙuriún da aka dangwala ɗan uwansa kamar yadda wani ɗan Jarida Norullah Noori ya shaidar. Yace ya so ya kai rahoton maguɗin gidan talabijin na Kandahar to amma abu ne mawuyaci.

" A matsayin mu na yan jaridu masu zaman kansu. bamu da damar zuwa mazaɓu a ƙauyuka, saboda haɗarin waɗannan wurare. Ina tsammanin ma dai babu ɗaya daga cikin jamián sa ido ko wakilan hukumar zaɓen da suka duba yanayin rumfunan zaɓe a faɗin ƙasar".

Mutane dai da dama a gundumomin kudanci kamar Kandahar da lardin Helmand basu fita ba a lokacin zaɓen saboda fargaba ta taɓarɓarewar tsaro da kuma barazanar yan Taliban. Aƙalla kashi biyu bisa uku na jamaár waɗannan yankuna zama suka yi a gidajensu suka ƙauracewa zaɓen. Mahammed Zaher daga Kandahar yace da muguwar rawa gwamma ƙin tashi domin zuwa wajen ba zai haifar masa da koma bai sai ɓacin rai saboda ya san cewa tabbas zaá aikata maguɗi.

" Yan Taliban sun razana mu domin an sami hare hare a wannan rana. Saboda haka ban bar kowa daga cikin iyalaina zuwa wajen zaɓen ba. Kuma ma wa zasu zaɓa ? tun da dai mun san a takarda rubutawa zaá yi cewa Karzai shine wanda ya lashe zaɓen".

Wani maáikacin wucin gadi a Jalalabad Abdul Mehdi wanda ya kaɗa kuriá ya kuma ganewa idanun sa, yace a mazaɓarsa baá yi maguɗi ba, amma kuma abin ya bashi mamaki yadda alaámura suka gudana a wasu mazaɓu. Yace yayi imanin baá yi zaɓe na gaskiya ba saboda abinda ya ji daga yan uwansa da kuma abokai game da maguɗi a sassa daban daban. Musamman yace a mazaɓar Jalalabad an yaudari mata waɗanda basu da cikakken Ilmi da masaniya kan yadda zasu kaɗa ƙuriá.

"A rumfunan zaɓe na mata magoya bayan ɗan takara kan gayawa matan wanda zasu zaɓa da inda zasu dangwala hannu a katin zaɓen. Dalili kuwa shine matan basu da ilmi ba zasu iya rarrabewa a tsakanin yan tarara ba".

Kasancewar baá gama tantance ƙorafe ƙorafen ba ya sa baá baiyana sakamakon ba a hukumance. Ya zuwa yanzu dai kwamitin karɓar ƙararrakin zaɓe yayi hukunci ne akan ƙararraki 16 daga cikin ƙorafe ƙorafe guda 2200 da aka shigar. Ana dai sa ran faɗin cikakken sakamakon zaɓen ne a ranar 17 ga wannan watan.

 • Kwanan wata 10.09.2009
 • Mawallafi Abdullahi Tanko Bala
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/JcTS
 • Kwanan wata 10.09.2009
 • Mawallafi Abdullahi Tanko Bala
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/JcTS