Rouhani ya bukaci Izraela ta shiga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya | Labarai | DW | 26.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rouhani ya bukaci Izraela ta shiga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya

Sabon shugaban Iran, ya nunar da cewar Izraela ce kadai kasar da bata cikin wannan yarjejeniya a yankin na gabas ta tsakiya.

Shugaba Hassan Rouhani na Iran ya yi kira ga Izraela, da ta hade a yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya. Ya yi wannan kiran ne a jawabinsa a taro na musamman kan nukiya a zauren MDD, a yayin da ake shirin farfado da tattauwar diplomasiyya kan nukiliyar Tehran. Rouhani ya ce abun takaici ne cewar, yunkurin shekaru 40 na kasa kasa wajen kawar da makaman nukiliya a yankin gabas ta tsakiya ya ci tura. A cewar sa kasar Izraela ce kadai bata cikin wannan yarjejeniya ta hana yaduwar makaman nukiliya a yankin, tare da jaddada bukatar ta hade ba tare da wani jinkiri ba.

Babban sakataren Majalisar Dunkin Duniya Ban ki-moon, ya fada wa mahalarta taron cewar, an samu ci gaba a 'yan shekarun da suka gabata dangane da kwance makaman nukiliya, da suka hadar da rufe cibiyoyin gwajin makamai da lalata wasu makaman a bangaren kasashe. Sai dai yace hakki ya rataya wuyan kasashen da ke mallakar makaman nukiliya na kare al'ummominsu daga barazanar makaman, sabodo illolinsu yafi amfaninsu yawa.

Fraimistan Japan Shinzo Abe, ya yi amfani da wannan taro wajen kira ga shugabannin duniya da su ziyarci Hiroshima da Nagasaki, domin gane wa idanunsu illolin amfani da wadannan makamai.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh