1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Zargin kashe masu zanga-zanga

Binta Aliyu Zurmi
November 20, 2019

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya yi ikirarin cewa sun samu nasara a kan masu zanga-zanga, inda ya dora alhakin abin da ke faruwa a kasarsa kan kasashen waje.

https://p.dw.com/p/3TNnD
Iran Protest Benzinpreise
Zanga-zangar adawa da karin kudin man fetur a IranHoto: FARS

Kafar yada labaran gwamnatin Iran din ce ta yada jawabin da shugaban kasar ya yi, a daidai lokacin da dubban mutane suka fantsama kan tituna domin yin zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati dangane da matakan da ta dauka na kara farashin man fetur.

Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam irinsu Amnesty International ke cewa sama da mutane 100 suka halaka a yankuna daban-daban na kasar, a kokarin murkushe masu zanga-zangar.