Ronaldo da Mourinho sun kaucewa haraji | Labarai | DW | 03.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Yan wasa sun tsara aucewa biyan haraji da gangan

Ronaldo da Mourinho sun kaucewa haraji

Wata badakalar kaucewa biyan haraji da jaridar Der Spiegel ta Jamus ta bankado ta nuna Christiano Ronaldo ya kaucewa biyan haraji na miliyoyin daloli.

Wasu kafofin yada labaran Turai sun wallafa abin da suka kira wani tsararren shiri na kaucewa biyan haraji da wasu shahararrun yan wasan kwallon kafa da masu horar da su suka yi. Yan wasan sun hada da Christiano Ronaldo dan wasan gaba na Real Madrid, da manajan kungiyar Manchester Jose Mourinho da kuma dan wasan tsakiya na Arsenal Mesut Ozil. Mujallar Der Spiegel ta Jamus ta ce Ronaldo ya tura kudi euro miliyan 75 kwatankwacin dala miliyan 80 zuwa wani asusun ajiya na banki a Swiss domin kaucewa biyan haraji.