Rodrigo Duterte ya yi rantsuwar kama shugabancin Pilipin | Labarai | DW | 30.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rodrigo Duterte ya yi rantsuwar kama shugabancin Pilipin

Bayan karbar madafun iko da wannan kasa ta Pilipin a fadar shugaban kasa, Duterte ya ce akwai rashin aminta da tsari na shugabanni a wannan kasa dan haka al'ummar kasar sun zaku su ga canji.

Philippinen Vereidigung des neuen Präsidenten Rodrigo Duterte

Rodrigo Duterte sabon shugaban kasar Pilipin lokacin rantsuwar kama aiki

Rodrigo Duterte ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban kasar Pilipin da ke zama shugaba na 16 a wannan rana ta Alhamis. Sabon shugaban dai a lokacin da yake jawabin kama aiki ya sha alwashi na ci gaba da yaki da miyagun laifuka, sannan ya gargadi ma'aikatan gwamnati da cewa ba zai lamunci cigaban cin hanci da rashawa ba a wannan kasa.

Bayan karbar madafun iko da Pilipin a fadar shugaban kasa, Duterte ya ce akwai rashin aminta da tsari na shugabanni a wannan kasa don haka al'ummar kasar sun zaku su ga canji.

Shi dai Duterte dan shekaru 71 tsohon magajin garin Davao babban birni na Mindanao a Pilipin ya kai kololuwa ta karbar shugabancin wannan kasa bayan zabe mai cike da cece-kuce saboda yadda a yayin kamfe ya rika bayyana kalamai na tsoratarwa kamar zai kashe dubban masu aikata miyagun laifuka da dai sauransu. Ana yi masa kallon kuma wanda zai iya watsi da batun kare hakkin bil Adama don ganin doka ta yi aikinta a kasar.