1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rintsaɓewar faɗa a Somaliya

August 25, 2010

faɗa na ci gaba da ƙazanta tsakanin dakarun gwamantin Somaliya da kuma mayaƙan sa kai na Al Shabbab.

https://p.dw.com/p/Ovml
Dakarun gwamnatin SomaliyaHoto: AP

Arangama na ci gaba da ƙamari tsakanin dakarun gwamantin Spmaliya da kuma masu tsananin kishin addinin musulunci na Al-Shabbab. Ɓangarorin biyu sun shiga kwana ta uku ta musayar harbe harbe da manyan makamai tsakaninsu da ya haddasa mutuwar fararen hula da dama. Kanfanin dillacin labaran Faransa wato AFP ya ce aƙalla mutane shida ne rokoki suka ritsa da su, yayin da wasu mutane 25 ke kwance a asibiti rai a hannu Allah.

Su dai mayakan sa kai na Al-Shabbab da ke da alaka da ƙungiyar Al-Qa'ida ta Usama Bin Laden, sun lashi takobin ganin bayan gwamantin riƙon ƙwarya ta Sherif Ahmed, da kuma rundunar wanzar da zaman lafiya ta AU da ke marawa gwamanti baya. Dukkanin bangarorin na biyu, wato Al-Shabbab da kuma gwamanti na iƙirarin samun nasara akan abokan gaba.

Mutane 65 aka tabbatar sun rasa rayukansu tun bayan ɓarkewan fada a kusa da fadan shugaban ƙasar ta Somaliya. Kashi 90 % na faɗin ƙasar ne ke hannun masu tsananin kishin addini na Al-Shabbab.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita. Abdullahi Tanko Bala