Rikicin Yemen na kara kazanta | Labarai | DW | 14.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Yemen na kara kazanta

Rahotanni daga kasar Yemen na nuni da cewa mayakan 'yan tawayen Houthi sun kwace iko da al-Hazm babban birnin gundumar al-Jawf.

Yaki ya dai-daita Yemen

Yaki ya dai-daita Yemen

Kwace birnin na al-Hazm da ke kan iyakar kasar da Saudiya na zuwa ne a dai-dai lokacin da dakarun rundunar taron dangi da Saudiya ke jagoranta ke ci gaba da luguden wuta a kasar a kokarin da take na fatattakar 'yan Houthi. Kwace iko da birnin na al-Hazm dai na zaman wata gagarumar nasara da 'yan tawayen suka samu kwana guda gabanin tattaunawar sulhu da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya domin bangarorin da ke yakar juna a Yemen din a birnin Geneva.

Wani mazaunin birnin na al-Hazm ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho cewa: a yanzu haka dakarun Houthi da kuma mayakan da ke goyon bayan tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh sun mamaye gine-ginen gwamnati a birnin.