Rikicin tsibirin Jaffna a Sri Lanka | Labarai | DW | 26.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin tsibirin Jaffna a Sri Lanka

A Sri Lanka sojoji 6 sun rigamu gidan gaskiya sannan akalla 4 sun samu raunuka lokacin da suka share wasu wuraren da ake boya lokacin yaki a yankin tsibirin Jaffna. Gwamnatin kasar ta zargi ´yan tawayen Tamil Tigers da fashewar bam din da ya rutsa da sojojinta. Sama da sojoji da kuma ´yan tawaye 600 suka rasa rayukansu sakamakon kazamin fadan da aka shafe makonni biyu ana yi a arewacin kasar ta Sri Lanka. A kuma halin da ake ciki Hukumomi a yankin sun fara rarraba kayan abinci ga al´umar yankin tsibirin Jaffna da ´yan tawaye suka yiwa kawanya. A jiya kungiyar agaji ta kasa da kasa wato Red cross ta tura jiragen ruwa guda biyu dake dauke da kayan agaji zuwa Jaffna. MDD ta yi kiyasin cewa mutane dubu 200 suka tsere daga yankin sakamakon wannan rikici tsakanin dakarun gwamnati da ´yan tawayen Tamil Tigers. Majalisar ta ce har yanzu wasu dubun dubatan ´yan gudun hijira na jiran a kai musu dauki.