Rikicin tsakanin mayakan Taliban da dakarun gwamnati a Afghanistan | Labarai | DW | 19.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin tsakanin mayakan Taliban da dakarun gwamnati a Afghanistan

´Yan sandan Afghanistan na ci-gaba da farautar ´yan tawayen kungiyar Taliban bayan fafatawa ta kwanaki biyu mafi muni tun bayan hambarad da gwamnatin Taliban a karshen shekara ta 2001. A cikin wannan makon mayakan Taliban sun tsananta hare hare akan dakarun ketare da na gwamnatin Afghanistan a daidai lokacin da sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar NATO suka isa a wannan kasa. Rundunar sojin Amirka ta ce ´ya´yan Taliban sun tsananta hare haren a kokarin su na dakushe duk wani goyon bayan da dakarun ketare ke samu daga al´umar Afghanistan. Daukacin ´yan kasar ciki har da shugaba Hamid Karzai na zargin Pakistan da haddasa rikicin baya bayan nan. To sai dai Pakistan wadda ita ma ta ke yakar mayakan Taliban da na Al-Qaida a nata bangaren na kan iyakar ta musantan wannan zargi.