Rikicin tawaye a Sri-Lanka | Labarai | DW | 01.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin tawaye a Sri-Lanka

Shugaban ƙasar Sri-Lanka, ya yi tayin zaman lahia, ga yan tawayenTamoul Tigers.

Shugaba Mahinda Rajapakse, ya buƙaci yan tawayen su koma tebrin shawara da gwamnati, muddun su na da shawara hakan.

Tantanwar ƙasrhe tsakanin ɓangarorin 2, ta cije a watan oktober na shekara bara, inda su ka watse baran-baran a birnin Geneva na ƙasar Suizland.

Daga wannan lokaci, ƙasar Sri-lanka ta ƙara durmuya cikin yanayin yaƙe- yaƙe, da tashe-tashen hankulla.

Shugabanin ƙungiyar Tamouls Tigers,, sun gitta sharaɗin dakarun gwamnati su daina kai hare-hare a yankunan su, kamin tantanawar, kazalika sunyi wasti da bukatar gwamnati ta tsagaita wuta.

Tun daga ɓarkewar wannan yaƙi a shekara ta 1974 zuwa yanzu,a ƙala mutane dubu 60, su ka rasa rayuka a ɓangarorin 2.

Yan tawayenTamouls Tigers na buƙatar samun yancin yankunan Arewa, da Arewa maso gabacin Sri-Lanka.