Rikicin tawaye a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 02.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin tawaye a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Kare jini biri jini tsakanin dakarun gwamnatin Bangui da 'yan tawayen Seleka.

'Yan tawayen Seleka na Jamuriya Afirka ta Tsakiya, sun amince su hau teburin shawara tare da gwamnatin Jamhuriya Afirka ta Tsakiya, sannan kuma sun yanke shawara daina darkakawa zuwa Bangui, babban birnin ƙasar.Jim kaɗan kamin wannan sanarwa, rundunar kwantar da tarzoma da ƙungiyar ƙasashen yankin tsakiyar Afrika, ta yi wa 'yan tawayen kashedi, game da aniyarsu su ta kai hari a birnin Bangui.

A birnin Libreville ne na ƙasar Gabon, ɓangarorin biyu za su tattanawa.Tunni 'yan tawayen sun baiyana buƙatar shugaba François Bozize ya sauka daga karagar mulki, kamar yadda kakakin Seleka Kanal Djouma Narkoyo, ya jaddada:

Muna kira zuwa gare shi ya sauka daga karagar mulkin Jamhuriya Afrika ta Tsakiya, domin kaucewa zubar da jinin al'umar ƙasa.Muna tsaye kan bakarmu game da wannan bukata.

Kusan wata guda kenan da 'yan tawayen Jamhuriya Afrika ta Tsakiya suka tada saban bore, kuma suka yi nasara ƙwace fiya da kashi 50 cikin ɗari na ƙasar daga dakarun gwamnati.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman