Rikicin tawaye a ƙasashen Afirka | Amsoshin takardunku | DW | 14.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Rikicin tawaye a ƙasashen Afirka

Kusan duk ƙasashen Afirka sun fuskanci rikicin tawaye, wasu sun warware shi wasun kuma na fama da shi har yanzu

Kasashe ƙalilan ne na Afrika wanda ba su yi fama da rikicin tawaye ba, ia yankin Afrika ta Yamma, ƙasashen da suka kuɓuta daga irin wannan rikici basu wuce biyar ba daga jimlar ƙasashe yankin 15, daga cikin su akwai , Ghana, Togo, Jamhuriya Benin, Burkina Faso,Guine Conakry, da Gambiya.

A ɓangaren yankin gabacin Afrika ƙasashen gaba ɗaya babu ƙasar da ba ta yi fama da rikicin tawaye ba, ko kamin samu 'yanci ko kuma bayan samun 'yancin kai.

A tsakiyar Afrika akwai ƙasashen Kamaru, da Gabon.

Sai kuma yankin kudancin Afrika akwai ƙasashen Malawi,Swaziland,Zambiya.

Sai kuma yankin arewacin Afrika ƙasashen da ba su taɓa fama da tawaye ba sune Tunisiya da Masar.

Kasashe ne yanzu su ke fama da 'yan tawaye a Afrika?

Akwai ƙasashe da dama wanda sun yi nasara warware rikicin tawayen, wasu tun da jimawa.

To amma a halin yanzu ƙasashe da ke fama da wannan rikici suna da yawa , ba za mu iya zana su duka ba saida mu taƙaita.

Mai zafi-zafi dai shine wanda kuma ya ke kanun labaran duniya shine na Jamhuriya Afrika ta Tsakiya da na arewacin Mali.Sannan kuma ga na 'yan tawayen M23 a Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo.Ga ƙasar Sudan da maƙwabciyarta Sudan ta Kudu, daɗa uwa uba Somaliya.

Sannan akwai wani daɗɗaɗen rikicin tawaye wanda ba aka cika zancen sa ba wato na tsaknain Marroko da Saharawi, inda hukumomin Marroko suka tsayi daka cewar wannan yanki mallakar su a yayin da sukuwa al'umar yanki suke ainayar da kansu a matasayin ƙasa mai cikkaken 'yanci.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal