Rikicin tawaye a ƙasar Tchad | Labarai | DW | 25.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin tawaye a ƙasar Tchad

Yan tawayen gabancin kasar Tchad, sun sha alƙawalin kiffar da shugaba Idriss Deby Itno.

Don cimma wannan buri, yan tawayen sun sake girka wani saban haɗin gwiwa da su ka raɗawa suna UFDD, wato Union des Forces pour la Democtarie et le Progres.

Wannan haɗin gwiwa, ya gama mafiyawan kananan ƙungiyon tawaye, masu adawa da shugaban ƙasar Tchad.

A sabin harin da yan tawayen su ka kai, sun mamaye yankunan Goz Beida, da Am Timan da ke kussa da iyaka da ƙasar Sudan.

Rundunar tsaron ƙasar France, da ke Tchad, ta sanar cewa yan tawayen, sun harbi jirgin ta, da wasu makaman masu dogon zango.

Shugaban haɗin gwiwar ƙungiyar UFDD, Jannar Mahamat Nuri, ya tabatara da wannan zance.

A hira da yayi da gidan Redio RFI, shugaban yan tawayenTchad, ya zargi France da bada tallafi ga dakarun gwamnati.

Idan dai ba amanta ba, a watan Aprul da ya wuce, saida yan tawaye su ka shiga birnin N´Djamena , amma dakarun gwamnati su ka furgaɗe su, tare da taimakon rundunar France.