1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Sudan na ci gaba da daukar hankali

Usman Shehu Usman
May 12, 2023

Masu shiga tsakani na duniya suna iya kokarinsu amma basu kai ga shawo kan shugabannin da ke yaki don samun tsagaita wuta mai dorewa ba

https://p.dw.com/p/4RHtF
Sudan EU richtet humanitäre Luftbrücke in den Sudan ein
Hoto: Amanuel Sileshi/AFP

Jaridar die tageszeitung a sharhinta ta ce, masu shiga tsakani na duniya suna iya kokarinsu amma basu kai ga shawo kan shugabannin da ke yaki don samun dawwamammiyar tsagaita wuta ba, tattaunawar ta zama kusan ta son rai daga ko wane bangare. Yanzu abun bukata shi ne tserar da rayukan mutane, kuma matakin farko na samun haka shi ne tsagaita wuta domin bada damar kai taimako ga mabukata. A baka dai babban hafsan sojojin Sudan Abdelfattah al-Burhan da shugaban mayakan RSF Hamdan Daglo Hametti, duk sun amince da tsagaita wuta, amma kuma a fagen daga musamman biranen Khartoum da Omdurman da sauransu labarin ya sha bamban. Don haka jaridar ke cewa idan har kowane bangare ya ci gaba da dagewa kan matsayinsa na rashin yin sassauci to babu inda kasar Sudan ta dosa illa kara fadawa cikin rami kai tsaye.

'Yan gudun hijirar Sudan a Chadi
'Yan gudun hijirar Sudan a ChadiHoto: Zohra Bensemra/REUTERS

A sharhinta Jaridar die Zeit ta ce kusan mutane 400 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Kuma a yanzu alkaluman wadanda suka mutu sai karuwa yake yi. Shugaban kasar ya sanar da zaman makoki na kasa baki daya kana ya sanar da matakan taimakon jinkai. Jaridar ta ci gaba da cewa iska mai karfi hade da zabtarewar kasa sun haddasa rufe kauyen Nyamukubi  baki dayansa. Gabanin haka ruwan sama mai karfi da aka yi a yankin Kivu da ke gabashin kasar ta Kwango ya haifar da tumbatsar koguna da koramu inda suka cika suka batse, abinda yasa ruwa ya yi ta kwarara cikin gidaje da gonaki. Kauyuka Bushushu da Nyamukubi duk ruwa ya tafi da su. A cewar wani jami'in gwamnatin adadin wadanda suka mutu sun haura mutane 400, yayin da ake ci gaba da zakulo wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.

Taimakon jinkai ga 'yan gudun hijirar Sudan
Taimakon jinkai ga 'yan gudun hijirar SudanHoto: Amanuel Sileshi/AFP

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung, ta ruwaito ne cewa ma‘aikatan bogi kimanin 150,000 gwamnati ta gano cikin sunayen ma'aikatan da ake biya duk wata. Jaridar ta ce wani bincike da aka wallafa, ya tabbatar cewa ko dai wadannan mutanen ana basu albashi basa zuwa aiki, ko kuma babu su kawai sunayen bogi ne ake biya. Rahoton yace bayan an bi diddigi, hukumar kudi da hukumar binciken ayyukan kudi, an gano kimanin mutane 53, 328 da ake biyansu sau biyu a wata, ma'ana dai ana maimaita sunayensu cikin tsarin albashi kuma suna karba sau biyu. A cewar gwamnatin Kwango, kasar da ke fama da dadadden rikici, wannan ba karamin asara ba ne gwamnati ki yi a duk wata yayin da take fama da basuka na kasashen duniya.

die tageszeitung ta yi waiwaye ne bisa ziyarar shugaban gwamnatin Jamus a gabshin Afirka, inda ta ce yayin da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya kwatanta Kenya a matsayin jagora wajen kare mahalli, a gefe guda masu fafutukar kare mahalli a kasar Kenya, suna sukar gwamnatin Nairobi da cewa gina tashoshin makamashi a kasar na shafar hakkin talakawa 'yan kabilar Massai, inda ake lalata musu mahalli. Kungiyoyin fafutuka na cewa yayin da kowa ke maraba da makamashin da ake sabuntawa da sauran makamashi marar gurbata muhallli, dole ne su jaddada kira ga Jamus da kasashen Tarayyar Turai kan hakkin 'yan kabilar Massai da ake lalata wa wurarensu na asali.