1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Sudan da Sudan Ta Kudu

December 2, 2012

Jami'an Sudan da Sudan Ta Kudu sun gana domin warware rigingimun dake tsakanin su

https://p.dw.com/p/16uS8
(L-R) Pagan Amum, south Sudan chief negotiator, South Sudan's President Salva Kiir, former president of Nigeria Abdulsalam Abubakar, Chief African Union mediator Thabo Mbeki, former Burundi president Pierre Buyoya and President of Sudan Omar Hassan al-Bashir meet during talks in Ethiopia's capital Addis Ababa September 24, 2012. Leaders from Sudan and South Sudan will meet on Sunday for the first time in a year to try to agree on border security so that South Sudan can start exporting oil again, a lifeline for both economies. REUTERS/Tiksa Negeri (ETHIOPIA - Tags: BUSINESS COMMODITIES POLITICS)
Hoto: Reuters

A Lahadinnan ne babban mai shiga tsakani na Sudan Ta Kudu  ya gana da manyan jami'an Sudan Ta Arewa domin warware matsalar da suke fuskanta wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma, wadda ta shafi tattalin arziki da kuma tsaro a tsakanin kasashen biyu dake makwabtaka da juna. Bayan ganawar, mai shiga tsakani na Sudan Ta Kudu Pagan Amum, ya shaidawa manema labarai cewar sassan biyu na kokarin hada-kai ne da nufin cimma maslahar aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma kimanin watanni biyun da suka gabata, domin anfanar sassan biyu da ma inganta sha'anin tsaro a tsakaninsu. Ya yi wannan jawabin ne kuwa, bayan ganawar daya yi tare da Nafie Ali Nafie dake zama mataimaki ga shugaba Omar Hassan al-Bashir.

Tunda farko dai, Amum ya gana da babban mai shiga tsakani daga bangaren Sudan Ta Arewa, kana ministan kula da harkokin tsaron kasar Abdelrahim Mohammed Hussein a wannan Asabar.

Idan za'a iya tunawa dai takaddama akan iyaka da kuma na albarkatun man fetur, ya jefa kasashen biyu cikin yaki, gabannin kulla wata yarjejeniyar zaman lafiyar da - a yanzu haka suke kokarin aiwatar da ita.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita        : Mohammad Nasir Awal