Rikicin Somalia | Labarai | DW | 15.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Somalia

A birnin Mogadiscio na ƙasar Somalia,a na ci gaba da ɓarin wuta tsakanin dakarun gwamnati da mayaƙan kotunan Islama.

A yau laraba rahotanin daga ƙasar sun ce a ƙalla mutane 10 su ka rasa rayuka, wanda su ka haɗa da yan sanda 5.

Tashe tashen hakulla sun ƙara tsamari a Somalia, tun lokacin da aka fara taron haɗin ƙasa, wanda mayaƙan kotunan Islama su ka ƙaurace masa.

Dr Hassan Osman na babbar asibitin Medina, dake Mogadiscio ya bayyana matsanacin halin da ake fuskanta a wannan birni a sakamkon rikicin.

Ƙungiyar taraya Afrika, ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Dunia, ta ɗauki matakan aika dakarun shiga tsakani a ƙasar Somalia, kamar irin yadda ta yanke shawara, a game da rikicin Darfur na ƙasar Sudan.