Rikicin Somalia da Ethiopia | Labarai | DW | 22.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Somalia da Ethiopia

Shugaban mayakan kungiyoyin Islama a Somalia yayi kira ga ´yan kasar da su daura damarar yin jihadi da kasar Habasha. Hakan dai ya zo ne kwana guda kacal bayan rahotannin da aka bayar cewar Habasha ta tura sojojinta cikin Somalia don ba da kariya ga gwamnatin wucin gadi mai samun goyon bayan MDD. Sheikh Hassan Dahir Aweys yayi wannan kira ne a wani jawabi da yayi ta gidan radiyo. Ya ce Habasha ta girke dakaru a mazaunin gwamnati dake birnin Baidowa don kare abin da bayana da cewa wata gwamnatin mulkin je-ka na yi-ka. Kungiyar kotunnan Islama ta shirya wata zanga-zangar kyamar Habasha a birnin Mogadishu.