Rikicin siyasar Tunisiya na ɗaukar sabon salo | Labarai | DW | 29.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin siyasar Tunisiya na ɗaukar sabon salo

Al'ummar Tunisiya na fargabar faɗawa cikin rikici mafi muni a tarihin siyasar ƙasar tun bayan da aka hamɓarar da mulkin shugaban kama karya Zine al Abidine Ben Ali

Wata jam'iyyar da ba ruwanta da addini, da ke cikin gwamnatin ƙawancen Tunisiya wadda jam'iyyar Ennahda ke jagoranta ta yi kira da a kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa a matsayin wani mataki wanda zai sassauta rikicin siyasar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, sa'o'i kaɗan kafin dakarun soji su killace dandalin da masu zanga-zanga suka yi arangama.

An yi ta rikici kan yunƙurin 'yan adawa na hamɓarar da gwamnatin ƙasar bayan da a makon da ya gabata aka yi wa wani ɗan siyasar ƙasar kisar gilla, wanda shi ne irinsa na biyu a tsukin watanni shidda. Sojojin dai sun killace dandalin Bardo da ke Tunis bayan da masu adawa da masu goyon bayan gwamnati suka jefa wa juna duwatsu.

Al'ummar Tunisiyar na fargabar ko tana faɗawa cikin rikici mafi muni ne a tarihin siyasar ƙasar tun bayan da aka hamɓarar da mulkin shugaban kama karya Zine al Abidine Ben Ali wanda aka tilasta masa yin kaura a shekarar 2011 bayan da guguwar sauyi ta yi sanadiyyar zanga-zanga a kusan dukkan ƙasashen Larabawa.

Jam'iyyar adawar dai ta yi watsi da duk wani yunƙurin gwamnati na sasantawa kuma ta yi kira da a rusa majalisar dokokin ƙasar mai mambobi 217, kuma a 'yan makonnin da suka gabata 70 daga cikinsu sun ajiye muƙamansu sun koma suna zaman dirshen a gaban shelkwatar majalisar. To sai dai Firaministan ƙasar ya ce za a gudanar da zaɓe kafin nan da watan Disemba idan Allah ya kai mu.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Muhammad Nasiru Awal