Rikicin Siyasar ƙasar Masar | Siyasa | DW | 13.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin Siyasar ƙasar Masar

Magoya bayan kudin tsarin mulkin ƙasar da masu yin adawa da shi na ci gaba da yin kampe gabannin zaɓen raba gardama

Bayan makwanni biyu ana kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Masar da yan adawar,daga ƙarshe dai al,amura sun fara lafawa bayan da yan adawar ƙasar suka amince da shiga kaɗa kuri,ar,ko da yake sun ce,za su kaɗa kuri,ar rashin amincewa da kundin da suka ce,ci gaban mai tonon rijiya ne,da zai ƙara maya da kasar baya.Koda an kaɗa kuri,ar amincewa da wannan kundin,to fa angudu ba a tsira bane,domin muddin ba a zauna kan teburin shawara an tattauna ayoyin dokar to da sauran rina a kaba.

Yan adawar su na ƙorafin cewar kudin tsarin mulkin zai iya kawo tarnaƙi ga aikin yan jarida

FILE - In this Friday, July 13, 2012 file photo, Egyptian President Mohammed Morsi speaks to reporters during a joint news conference with Tunisian President Moncef Marzouki, unseen, at the Presidential palace in Cairo, Egypt. Egypt’s Islamist president may hail from the fiercely anti-Israeli Muslim Brotherhood, but in his first major crisis over Israel, he is behaving much like his predecessor, Hosni Mubarak:. He recalled the ambassador and engaged in empty rhetoric supporting Palestinians. Mohammed Morsi is under pressure at home to do more but he is just as wary as Mubarak about straining ties with the United States. (Foto:Maya Alleruzzo, File/AP/dapd)

Shugaba Mohamed Musi

Yawancin masu adawa da kundin suna ƙorafi kan sanya ayoyin dokkoki dak ewa yan jarida tarnaki,da kuma nuna wa mata da yara kanana wariya,yadda kundin ya amince da aurar da yara yan mata kafin cika shekara 18,batun da kungiyoyin mata suka ce,ba shi da banbanci da yiwa yara kananan fedey,kamar yadda kiristocin ƙasar ke cewa,kundin ya zake wajen cusa shari,ar musulunci a dukkan ɓangarorinsa.Su kuwa yan' gurguzu da ke da sassaucin ra,ayi cewa suke,kundin zai mayar da duk shugaban da za,a zaɓa ya zama mai mulkin fir,aunanci na kama karya..

Babu alamun daidaita wa tsakanin sasan biyu ko bayan zaɓen

Anti-Mursi protesters run for cover during clashes with riot police at Tahrir Square in Cairo November 27, 2012. Opponents of President Mohamed Mursi rallied in Cairo's Tahrir Square for a fifth day on Tuesday, stepping up calls to scrap a decree they say threatens Egypt with a new era of autocracy. REUTERS/Ahmed Jadallah (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)

Masu adawa da kudin tsarin mulki

Yanzu kam a Masar murna ta fara komawa ciki,domin wannan kundin da za,a gabatar zai kafa gwamnatin masu tsatstsauran ra,ayin islama ne data dara mulkin kama karya irin na sojoji muni,Mursi da muƙarraban sa ba za su iya mulkar Misarawan da ke ƙisharwar yanci ba ,sai ta hanyar mulkin fir,aunanci da kama karya..Wasu kuwa da ke ci gaba da yin zaman dirshan a farfajiyar fadar shugaban ƙasar da kuma dandalin Tahreer,fushin su suka nuna da gamayyar yan adawar da har ta amince da shiga kaɗa kuri,ar domin a ganin su,yin hakan amincewa da shugabancin shugaba Mursi ne da kuma shi kan sa kundin a fakaice.A daura da haka,masu goyan bayan shugaban na ci gaba da yin kamfen ɗin wayar da kai kan yan Kasar su futo kwan su da kwarkwatar su don kada kuri,ar amincewa da kundin.Tuni dai yan kasar dake ƙetare suka fara kaɗa kuri,un su,yadda su kuma yan cikin gida zasu fara kaɗa nasu ƙuri,un a ran asabar.

Mawallafi: Mahamud Azare Yaya
Edita : Abdourahamane Hassane

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

.

Sauti da bidiyo akan labarin