1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Somaliya: Rikicin siyasa na kamari

December 28, 2021

Dakatarwar da Shugaba Mohamed Abdullahi Farmajo ya yi wa Firaminista Mohamed Hussein Roble kan zargin kitsa masa juyin mulki, ya janyo fargabar barkewar rikicin siyasa.

https://p.dw.com/p/44v1m
Somalia Präsident Farmajo Premierminister Roble
Hoto: Abdirahman Yusuf/AFP/Getty Images

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, ya ce ya shaida dakaru dauke da makamai na rangadi a cikin birnin Mogadishu. Wannan rikici dai ya sanya al'umma a ciki da wajen Somaliyan nuna fargaba kan zaman doya da manjar da ke ci gaba da daukar sabon salo a tsakanin shugaban kasa da firaministan nasa. 

Shugaban kasar da firaministan nasa sun jima suna samun sabani, sai dai ana ganin rashin jituwarsu ta baya-bayan nan ka iya jefa kasar cikin rikici na siyasa ganin yadda ake ci gaba da samun jinkiri wajen gudanar da zaben shugaban kasa.

Sashen kula da harkokin Afirka na Ma'aikatar Harkokin Wajen Amirka, ya sanar da cewa akwai bukatar kai zuciya nesa, domin kar lamarin ya dakile aniyar kasar ta samun zaman lafiya mai dorewa.