Rikicin siyasa a kasar Kote Divoire | Labarai | DW | 31.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin siyasa a kasar Kote Divoire

Ranar jiya ne a kasar Kote Divoire wa´adin shugaba Lauran Bagbo bisa karagar muklkin kasar ya kai karshe.

Sabanin yada a ka zata, ba a fuskanci tashe tashen hankulla ba masu yawa.

A Abijan babban birnin kasar, magoya bayan jam´iyun adawa sun shirya zanga zangar neman saukar Lauran Bagbo daga karagar mulki.Saidai jami´an tsaro su ka tarwatsa su.

A manyan biranen arewancin kasar da ke cikin hannun yan tawaye, mutane sun amsa kiran shirya zanga zangar.

A birnin Buwake, a kalla mutane dubu 10, su ka fito bisa titina, don nuna kin jinnin shugaban kasar Kote Divoire.

A yammacin jiya, Lauran Bagbo ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana wajibcin tsayawar sa, bisa kujera mulki, ya kuma yi fatan shirya zaben shugaban kasa kamin karshen saban wa´adin shekara guda, da Majalisar Dinkin Dunia ta bada.

Ya zargi yan tawaye da yin kafar angullu ga yunkurin cimma zaman lahia a kasar Kote Divoire.

Bagbo ya alkawarta nada saban Praminista nan da lokaci mai zuwa.

Jim kadan kamin jawabin na sa, kungiyar yan tawaye ta FN, ta sannar nada madugun ta ,Guillaume Soro a matsayin saban Praministan rikwan kwarya.

A nasu bangaren kawacen jam´iyun adawa sun jaddada kin amincewa da Lauran Bagbo ya ci gaba da zama shugaban kasa, sun kuma ,kiri wata gagaramar zanga zanga ranar talata mai zuwa, a fadin kasa baki daya.