1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a kasar Iraqi

March 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5s

Yayin da shugabannin siyasa a Iraqi ke fafutukar kafa sabuwar gwamnatin hadin kann kasa, a waje guda kuma rigingimun dake faruwa na kara tauye wannan yunkuri da kuma ke kara jefa kasar cikin mawuyacin hali. Shugaban kasar jalalal Talabani, tare da wakilan kurdawa da sauran bangarorin adawa sun aike da tawaga domin saduwa da jagoran addini Ayatollah Ali al Sistani don sa baki cikin lamarin. Shi dai ayatollah al Sistani na da kima wajen alúmar kasar inda a baya ya taimaka wajen ganin zaben da aka yi a kasar ya gudana.

A waje guda kuma Amurka ta musanta rahoton da wata jarida ta Britaniya ta buga dake baiyana cewa Amurka Britaniya na shirin janye sojojin su daga Iraqi a farkon shekara mai zuwa. Babban hafsan sojin Amurka Janar Peter Pace Amurka zata janye dakarun ta 133,000 dake kasar Iraqin ne bayan an tabbatar da cewa sojojin Iraqi sun sami cikakken horo da kwarewa da zasu iya tafiyar da harkokin tsaron kasar su. Yace ko kadan labarin da jaridar ta buga ba gaskiya ba ne.