Rikicin siyasa a DRC | Labarai | DW | 29.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin siyasa a DRC

A wani saban bori na siyasa, a Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo, yan Majalisar dokokin yankin Kivu, sun ƙauracewa Majalisar.

Sun gita sharaɗin komawa kan kujerun su ,da tabbatar da tsaro a yankin Kivu, da ke fama da yaƙe- yaƙe.

Yan majalisar sun zargi gwamnatin Joseph kabila, da rashin taɓuka komai, ta fannin magance matsalolin tsaro a Kivu.

A watan da ya gabata, hukumar Majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da kare yancin bil Adama,ta ja hankalin gwamnatin Kinshasa, a game da cin zarafin yaya mata, a wannan yanki.