Rikicin shugabanci a PDP ya raba jam′iyyar a Kano | Siyasa | DW | 04.09.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin shugabanci a PDP ya raba jam'iyyar a Kano

Bayan da aka sanar da rushe shugabanci na jam'iyyar PDP da mika shi a hannun mafi akasari magoya bayan Rabiu Kwankwaso rikici ya barke tsakanin magoya bayan gida biyu inda magoya bayan Ibrahim Shekarau suka nuna turjiya.

Tun da fari dai an jiyo Sule Yau Sule da ke magana da yawun tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau na cewa tsohon gwamnan ya fice daga jam'iyyar PDP mai adawa, wannan dai ya sanya magoya bayan na Shekarau suka nuna cewa su kam duk inda jagoran nasu ya sa kafa za su bishi inda tuni wasu suka fara hassashen cewa zai koma jam'iyyar APC mai mulki.

Nigeria Ibrahim Shekarau Präsidentschaftskandidat

Tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau

'Yan siyasa dai a Kano Arewa maso Yammacin Najeriya kamar Musa Ilyasu Kwankwaso da ke zama kwamishina a jihar na masu ra'ayin cewa dama sun san za a rina kasancewar sun yi amanna cewa ba za a taba zama a rumfa guda daya ba tsakanin tsofaffin gwamnonin na Kano wato Malam Shekarau da Rabiu Kwankwaso.

A nasa bangaren tsohon gwamna Malam Shekarau ya ce lokaci ne zai nuna matsayar da suka dauka kan inda suka nufa a game da wannan takaddama da ta barke a PDP.

Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso

Manazarta a harkokin siyasa a jihar ta Kano dai na cewa sauya sheka da 'yan siyasa ke yi ba a bu ne mai alkhairi ba ga makomar kasar, kasancewar jagororin na siyasa sun fi mayar da hankali kan bukatar kansu ba ta talakawa magoya bayansu ba.

Sauti da bidiyo akan labarin