Rikicin nuklear kasar Iran | Labarai | DW | 14.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin nuklear kasar Iran

Gwamnatin kasar Iran, ta jaddada aniyarta, ta ci gaba da ayyukan samar da makashin nuklea, batun da har yanzu, a ke kai ruwa rana a kana sa, tsakanin Iran din, da kasashen masu fada aji a dunia.

Idan ba a manta ta ba, kungiyar gamayya turai, da Amurika, sun samu nasara ciwo kan hukumar yaki da yaduwar makaman nuklea, ta kasa da kasa, da gurfanar da Iran gaban komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia.

A satin da ya gabata, kasar Rasha da ke goyan bayan Iran, ta bukaci shiga tsakani, domin warware takkadamar.

Bangarorin 2 su yanke shawara tantananawa, daga 16 zuwa 20 ga watan da mu ke ciki.

Shima ministan harakokin wajen China, yayi hanunka mai sanda,ga turai da Amurika, tare da shawarta su, su koma shawarwari a game da matsaklar ta kasar Iran.

A sakamkon ganawar da a kayi yau, a fadar Kremblin ta birnin Mosko, tsakanin shugaba Vladmir Putin na Rasha,da pramninstan Fransa Dominique de Villepin, sun rattaba hannu akan watza sanarwa ta hadin gwiwa , inda su ka cimma yarjejeniya a kan wajibcin warware takadamar cikin ruwan sanhi.