1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta dauki matakai a kan Mali

Salissou Boukari LMJ
July 28, 2020

Shugabannin kasashen ECOWAS ko CEDEAO sun yi wani zama na gaggawa ta bidiyo a kan rikicin siyasar kasar Mali, inda suka dauki matakai har shida a kokarin daidaita rikicin siyasar Malin.

https://p.dw.com/p/3g4QA
Krise in Mali | ECOWAS | Macky Sall und Ibrahim Boubacar Keïta
Shugaba Macky Sall na Senegal da takwaransa na Mali Ibrahim Boubacar KeïtaHoto: Présidence du Mali

'Yan majalisar da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO din ta bukaci su yi murabus dai har su 31, a matsayin guda daga cikin matakan shida da shugabannin kungiyar suka dauka, rahotanni sun nunar da cdwa suna cikin wadanda 'yan adawa suka bayyana cewa ba a zabe su bisa ka'ida ba. Tuni dai jama'a suka fara tofa albarkacin bakunansu a kan wannan mataki da kungiyar ta Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ta dauka.

Baya ga batun murabus din 'yan majalisar dokokin da kotun tsarin mulkin kasar ta Mali ta sakasu a matsayin coge, akwai kuma batun ita kanta kotun tsarin mulkin yadda ya kamata a sake zaben sababbin mambobinta da batun kafa gwamnatin hadin kan kasa cikin gaggawa, wanda tuni aka soma da kafa sabuwar gwamnatin da batun kafa kwamitin bincike kan kashe-kashen da aka yi na masu zanga-zanga da kuma kafa wani kwamiti da zai bi matakan sau da kafa, sannan da daukan matakin hukunci ga duk wasu da za su hana ruwa gutu wajen aiwatar da wannan umarni na ECOWAS.

Mali Unruhen Protest Menschen auf den Straßen Polizeigewalt
Zanga-zangar kin jinin gwamnati a MaliHoto: Reuters/S. Ag Anara

Sai dai da yake magana kan wannan batu, Nassirou Saidou shugaban kungiyar Muryar Talaka a Nijar da ke bibiyar lamarin kasar ta Mali sau da kafa, ya ce ECOWAS ta yi abun da ba shi ya kamata ta yi ba. Koda yake a ta bakin Sahanine Mamadou mai sharhi kan harkokin siyasa a Jamhuriyar Nijar, matakin da CEDEAO ta dauka ya dace domin kuwa hakan idan aka yi amfani da shi zai kare wani tashin hankalin da ba za a iya sanin karshensa ba.

Sai dai daga bangaran 'yan kasar ta Mali da ke zaune a Jamhuriyar ta Nijar wadanda ke goyon bayan sauke shugaban kasar ta mali daga kan mulki irinsu Maiga Issifi Maiga da ke a matsayin dan gudun hijirar kasar Mali a Nijar kuma wakilin jam'iyyar siyasa ta SADI masu fafutukar ganin an samu sauyi tafiyar da harkokin jagoranci a kasar ta Mali. Sakamakon taron na ECOWAS kan Mali ya raunana musu zukata. Abin jira a gani dai shi ne matakin da 'yan kasar ta Mali za su dauka a nan gaba, wanda ka iya kasancewa zai bude wani sabon babi na rikici tsakaninsu da kungiyar ECOWAS da ta ce tana fa da sandar hukunci ga duk wani da ya bijirewa matakan nata.