Rikicin makiyaya da manoma ya yi tsamari a Nijar | Siyasa | DW | 28.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin makiyaya da manoma ya yi tsamari a Nijar

Tashin hankalin a wannan karo a wani yanki na Damagaram na Nijar manoma sun kama shanu da wasu dabbobi a matsayin fansa.

A yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar daruruwan manoma ne suka tashi a tutar babu sakamakon mamayar gonakin noma da garke-garke daga makiyaya a karamar gundumar Damagaram Takaya, Tuni dai hukumomi suka kame dabbobin makiyayan da suka aikata barnar don rama cimakar da dabbobin suka ci. Wanan barna dai ta zo kafin  hukumomi su bada wa'adin sakin gonakin noma a hukumance.

Flash-Galerie Tuareg (AP)

Wanan halin tsaka mai wuya dai ya ritsa ne da manoman karamar gundumar Takaya daya daga cikin kananan gundumomi goma na baya-bayan nan sabbin girkawa a yankin Damagaram. Wasu manoma na barin 'ya'yansu su kwana a gonaki saboda tsaro.


To sai dai a cewar daya daga cikin matan makiyaya da ta ki amincewa a dau muryarta ta na kokarin tattara dabbobin da suka watsu a gona ba su da zabi biyayya suke wa mazajensu.

Hukumomi sun kame dabbobi masu yawa da suka hada da tumaki da shanu a wani mataki na biyan diyya ga manoman. Har izuwa lokacin hada wanan rohoto dai  kokarin da wakilin DW a Damagaram ya yi  don jin ta bakin wakilan makiyaya hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Sauti da bidiyo akan labarin