Rikicin Libiya na shafan diplomasiya | Labarai | DW | 27.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Libiya na shafan diplomasiya

An kwashe ma'aikatan diplomasiyan Amirka daga Libiya saboda rashin tsaro

Kasar Amirka ta kwashe ma'aikatan ofishin jakadancin kasar da ke birnin Tripoli na kasar Libiya saboda cigaba da kai ruwa rana da ake samu tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai.

A wannan Asabar da ta gabata aka kwashe ma'aikatan zuwa kasar Tunisiya. A makonnin biyu da suka gabata fada ya zafafa tsakanin tsagerun da ke dauke da makamai abin da ya yi sanadiyar lalata filin saukan da tashin jiragen saman birnin. Shekaru biyu da suka gabata aka hallaka jakadan Amirka a birnin Bengazhi na kasar ta Libiya da wasu ma'aikata Amirkawa uku.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba