Rikicin Kwango na daukar sabon salo | Labarai | DW | 05.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Kwango na daukar sabon salo

Dubban 'yan kasar ta Kwango ke kauracewa matsugunnensu sakamakon barkewar rikici a dalilin takaddama tsakanin kabilu da neman mallakar albarkatun kasa

Ƙungiyoyin agaji sun ce aƙalla muatne 70 suka mutu wasu dubban kuma suka ƙauracewa matsugunnensu bayan da aka shafe kwanaki ana gumurzu tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnati a gabashin Jamhoriyar demokraɗiyyar Kwango.

Rikicin tsakanin dakarun sojin da 'yan ƙungiyar tawayen APCLS wanda aka fara a makon da ya gabata a garin Kitchanga shine rikicin baya-bayan nan a jerin rikice-rikicen da suka addabi wannan yanki da ke fama da illolin ƙabilanci da taƙaddama kan albarkatun ƙarƙashin ƙasa

Waɗannan rigingimu na nuna irin sarƙaƙiyar da faɗace-faɗacen na gabashin Kwango, musamman ma batun jagoranci da mallakar albarkatun ƙarƙashin ƙasa inda ake zargin dakarun kowani gefe da amfani da miyagun ƙwayoyi da ma fyaɗe da kuma kisan fararen hulan da basu ji basu gani ba.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mohammed Awal Balarabe