1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar kasuwancin China da Amirka

Abdul-raheem Hassan
July 6, 2018

Shugaba Donald Trump ya jaddada fara aiwatar da matakin sabbin haraji a kan kayayakin gyaran jirage da komfuta da kasar China ke shigarwa Amirka.

https://p.dw.com/p/30vCU
USA Washington - Donald Trump verhängt Strafzölle gegen China
Hoto: Reuters/J. Ernst

A wani mataki na bude sabon babin yakin kasuwaci tsakanin Amirka da China da ke zama kasahe mafi girman tattalin arziki, Amirka ta ce ba ja da baya kan matakinta na sanya harajin dala biliyan 34 kan wasu kayyakin da kasar China ke dillancinsu a Amirka.

Sai dai jami'an Chinan na ganin matakin a matsayain takalar fada da neman haddasa yakin kasuwacin tsakanin aksashen biyu, kasar Chinan ta ce zata dau matakin ramuwar gayya a kan kayan amfanin gona da Amirka ke shigar wa kasarta.

Masana na fargabar tsamin dangantaka da ke tsakanin Amirka da China zai durkusarda tattalin arzikin kasashen biyu, tare da haddasa tafiyar hawainiya a harkokin cinikayya da kasuwanci a duniya.