1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kasar Ivory Coast

October 30, 2005
https://p.dw.com/p/BvNI

Sojojin gwamnati a Ivory Coast wato Kodivuwa sun tsananta sintiri da suke yi a birnin Abidjan a yau lahadi a daidai lokacin da daruruwan ´yan adawa da shugaba Laurent Gbagbo ke wani taron gangami don yin kira da shugaban da ya sauka daga karagar mulki bayan cikar wa´adin shugabancinsa da 12 dare. Ana fargabar yiwuwar barkewar wani rikici a kasar dake yammacin Afirka a yau lahadi lokacin da wa´adin shekaru 5 na shugabancin Gbagbo ke karewa. Tun bayan barkewar yaki basasa a cikin shekara ta 2002 kasar ta rabu gida biyu, inda ´yan tawaye ke rike da arewaci yayin da gwamnati kuma ke iko a kudancin kasar. Duk wani shirin zaman lafiya na MDD wanda ya kyale shugaba Gbagbo ya ci-gaba da mulki har zuwa watanni 12 nan gaba lokacin da za´a gudanar da zabe, ´yan adawa sun ce ba zasu amince da shi a matsayin shugaban kasa ba bayan 12 daren yau lahadi. Wasu matasa sun yi barazanar gudanar da zanga-zangar tilastawa Gbagbo ya sauka.