1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya ya jefa al'umma cikin ukuba

October 17, 2013

Kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta Doctors Without Borders ta nemi kasashen duniya su hanzarta agazawa Jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/1A1mg
Soldiers patrol on an armoured vehicle as people demonstrate for the restoration of peace within the country on September 2, 2013 in Bangui. AFP PHOTO / PACOME PABANDJI (Photo credit should read PACOME PABANDJI/AFP/Getty Images)
Hoto: P.Pabandji/AFP/GettyImages

A cikin wata sanarwar da kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta fitar, ta ce dubun dubatan mazauna kauyuka ne suka tserewa matsugunansu sakamakon hare haren da suke fuskanta, a daidai lokacin da dakarun gwamnati ke ci gaba da fafatawa da kungiyoyin da ke dauke da makamai.

Jami'ar kungiyar a Jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya Ellen Van der Velden, ta ce galibin mutanen da suka tsere wa fadan dai na yin gararamba ne a cikin daji, kuma suna fuskantar hatsarin kamuwa da cututtuka irin su Malariya, wadda dama ke kan gaba wajen haddasa kissan mutane a kasar.

Rikicin baya bayan nan dai ya fi tsananta ne a garin Bossangoa da ke zama mahaifar tsohon shugaban kasar Farancoir Bozize, wanda 'yan tawayen kungiyar Seleka suka kifar da gwamnatinsa, kuma jagorar kungiyar, Michel Djotodia ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa, kana a yanzu magoya bayan tsohon shugaban ke ta yin fito da fito da kungiyar ta Seleka, wanda ya janyo kona gidaje da dama a yankin, game da asarar dukiya mai dimbin yawa, lamarin da a cewar wani mazaunin yankin ya tilstawa jama'a shiga daji:

Ya ce " Har yanzu suna cikin daji. Akwai mutane da dama da ke cikin dajin, wadanda ke rayuwa da ganyen rogo."

Medical staff of Medecin Sans Frontieres (Doctors without Borders) prepare an injection as injured people sit on beds at a community hospital in Bangui, on March 29, 2013. Hospitals in the coup-hit capital of the Central African Republic overflowed with injured people and tens of thousands faced hunger as the humanitarian situation in the country worsened just days after rebels seized power. AFP PHOTO / SIA KAMBOU (Photo credit should read SIA KAMBOU/AFP/Getty Images)
Hoto: Sia Kambou/AFP/Getty Images

Rikicin Jamhuriyyar Afirka Ta tsakiya na kara janyo mutuwar jama'a

Akalla mutane 100 ne suka mutu sakamakon fadan da ya afku a kauyen na Bossangoa cikin watan Satumban nan, bayan wadanda ke fama da matsalar yunwa a cikin dajin.

Yakin na ci gaba da wanzuwa a tsakanin kungiyoyin da ke dauke da makamai da kuma 'yan tawayen Seleka ne, duk kuwa da cewar, shugaba Djotodia ya sanar da rusa kungiyar bayan juyin mulkin da ta yi wa Bozize a ranar 24 ga watan Maris, kana ya karbi rantsuwar kama aiki a cikin watan Augusta, inda wani dan kasar da rikicin ya rutsa dashi ya ce har yanzu ba su gani a kasa ba dangane da furucin na Djotodia.

Ya ce " 'Yan Seleka suna dauke da makaman gargajiya irinsu Adda da Gatari suna bin gidajen mutane suna kokkonawa."

Residents, who had found refuge in a nearby forest during clashes, go about their daily chores on October 8, 2013 after returning to Bangassou. The Central Africa Republic has been shaken by a recent increase in clashes between ex-rebels of the Seleka coalition that led the coup, who are Muslim, and local self-defense groups formed by rural residents who are Christian, in common with around 80 percent of the population. The poor but mineral-rich nation was plunged into chaos when a coalition of rebels and armed movements ousted longtime president Bozize and took the capital Bangui in March. AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO (Photo credit should read ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images)
Daya daga cikin cibiyoyin da ke agazawa jama'aHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Neman tallafin kasashen duniya domin warware rikicin

A cewar kungiyar Doctors Without Borders, mutane da dama ne ke begen samun tallafi sakamakon ukubar da suka shiga, domin a cewarta hatta a Bosangoa kadai akwai kimanin mutane dubu 30 da ke cikin tsananin bukatar, inda wasunsu ke samun tallafi daga cocin katolika da ya samar da wata cibiya a garin, yayin da wasu kuma ke samun mafaka ko dai a makarantu ko a sibitoci ko kuma a wani karamin filin jirgin sama da ke yankin. Daya daga cikin wadanda ke cibiyar ya yi karin haske:

Ya ce "An barmu kamar karnuka masu jin yunwa. Muna tare da 'ya'yanmu, kuma kowa na jin yunwa. Ba ma iya zuwa gona, kuma amfanin da muka samu duk an la'la'ta."

Yakin dai na neman rikidewa ya koma a tsakanin Kiristoci masu rinjaye a kasar da kuma Musulmi, tare da zargin kasashen Sudan da Chadi da tallafa wa 'yan tawayen, zargin da kuma Chadin ta yi watsi dashi.

A makon jiya ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi na'am da wani kudirin da ya tanadi tallafa wa dakarun wanzar da zamnan lafiyar da Kungiyar Tarayyar Afirka ta tura kasar, wadda ke fama da matsalolin kudi da kayayyakin aiki, domin tabbatar da cewar ta yi aikinta yadda ya kamata.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir awal