Rikicin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango | Labarai | DW | 29.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango

Sojojin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango sun yi bata kashi da masu neman ballewa na yankin Katanga a birnin Lubumbashi da ke zama na biyu a girma a kasar.

Dakarun Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango sun fafata da wasu 'yan bindiga a kusa da wani rumbun ajiye makamai da ke Lubumbashi, birnin na biyu mafi girma a kasar. Ba a dai bayyana yawan mutane da suka rasa rayukansu ko kuma suka jikkata a wannan artabu ba. Amma kuma wata kafa ta soji da kuma shaidu sun bayyana wa kanfanin dillancin labaran Faransa cewar bangarorin biyu sun shafe sa'o'i uku na daren wannan Litinin (28.10.13) suna bata kashi tsakaninsu a tsakiyar birnin da ke cikin yankin kudu maso gabashin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango.

Hukumomin wannan kasa suka ce masu fafutukar ballewa na yankin Katanga ne suka kai wa sojojin hari kafin daga bisani su mayar da martani don kare kansu. 'Yan aware na Bakata Katanga, sun saba kai hare-hare a runbun ajiye makamai na sojoji. Ko a watanni bakwai da suka gabata ma dai sai da suka yi fito na fito da sojoji a kusa da ofishin gwamnan Lubumbashi inda mutane 23 suka rigamu gidan gaskiya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Saleh Umar Saleh