1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Gazali Abdou Tasawa
May 2, 2017

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tana sake shiga mawuyacin hali, sakamakon karuwar tashe-tashen hankula tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai.

https://p.dw.com/p/2cEm7
Zentralafrikanischen Republik Bangui - Militär durchquert Strasse
Hoto: picture-alliance/AA/N. Talel

Kungiyoyin agaji na kasa da kasa sun bayyana damuwarsu dangane da mawuyacin halin rayuwar da al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke ciki a yanzu haka, sakamakon fadan da kungiyoyin tawaye masu gaba da juna suka share shekaru suna yi a kasar.

Dubban 'yan kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wadanda suka kaurace wa gidajensu sakamakon yaki, suka fara koma wa matsugunnansu, sai dai duka suna mara bayan ne ga kungiyar tawayen addini da suke bi, inda Musulmi ke bayan kungiyar tawayen Seleka yayin da Kiristoci ke bayan kungiyar tawayen Anti-Balaka. Kungiyoyin dai na ci da gumin mabiyansu, inda suke karbar kudade a wajen mutane domin ba su kariya su da kadarorinsu da suka yi saura. Kanal Goumou Passy na kungiyar tawayen Kiristoci ta Anti-Balaka ya yi karin bayani a kan matakan da suke dauka:


"Muna cikin yaki ne kuma kowa na da irin tasa fasahar domin samun nasara. Dan haka mu a yanzu mun dauki matakin datse hanyoyin shigo da kayan agaji har zuwa wani lokaci"

Zentralafrikanische Republik - Blauhelmsoldat in Bangui
Hoto: Getty Images/AFP/G. Guercia

Makwanni hudu kenan da Kanal Passy da mayakansa suka haramta shigo da kayan abinci na agajin jama'a a yankin Koui, lamarin da ya haddasa tabarbarewar yanayin rayuwa a yankin. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta zargi Kwamanda Sidiki Abass daya daga cikin shugabannin kungiyar tawayen Musulmi ta Seleka a garin na Koui, da cin zarafin dan Adam ta hanyar azabtar da mutane da yi wa mata fyade. Sai dai ya musanta zargin yana mai cewa:

"Ba mau samun kariya a inda muke. Ko da yaushe 'yan bindiga da 'yan tawayen Anti-Balaka na kawo mana hari. Kuma gwamnati ta ki ta yi wani abu a kai, dan haka dole mu dauki matakin kare kanmu"

Sai dai daga nashi bangare Adamou Dawda Yaya magajin garin na Koui ya ce suna goyon bayan kasancewar kungiyar ta Seleka a garin nasu, wadda ya ce da babu ita da tuni 'yan tawayen Anti-Balaka sun wargaza garin. Shugabanni addini a garin na Koui dai a yanzu haka, na aiki kafada da kafada da ma da rubuta wata wasika ta hadin gwiwa inda suka yi kira ga kungiyoyin tawayen da su dakatar da fadan da suke yi a tsakaninsu da sunan addini, domin ganin an bai wa Musulmi da Kirista damarci gaba da rayuwa tare cikin kwanciyar hankali kamar yadda suka kasance a baya.