Rikicin iraki | Labarai | DW | 06.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin iraki

Binciken da aka gudanar akan tsohon shugaban kasar Iraki sadam Hussein,da kunma takardun da aka kwace daga gwamnatinsa bayan mamayen kasar da Amurka tayi wa jagoranci,na nuni dacewa gwamnatinsa bata da wata alaka da kungiyar alqaeda,inji rahotan jaridar washinton post.Wannan rahotan dai ya karyata dukkan dalilai da gwamnatin shugaba Bush na Amurka ya gabatar, amatsayin dalilansa na kaiqwa irakin farmaki da karfin soji.Rahotan jaridar dai na nuni dacewa sakamakon binciken da sashin tsaro na Amurka da hukumar bincike ta CIA suka gabatar bayan kifar da gwamnatin mareigayi sadam na tabbatar dacewa,gwamnatinsa bata da wata alaka da kungiyar Alqaeda ,wadda ake zargi da harin kunar bakin waken 11 ga watan satumba a Amuirka a shekarata 2001.